A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, muna gabatar muku da jerin darussan Mahdawiyya mai taken "Zuwa Ga Al'umma Mai Manufa", da nufin yada koyarwa da ilimin da ke da alaƙa da Imamuz Zamani (A.T.F.S).
Shin "Tsarin Imamanci" ya zo ƙarshe ne da ƙarewar lokacin Gaiba as-Sughra da farkon Gaiba al-Kubra, sannan sai bayan bayyanar Imam Mahdi (A.S) za a sake kafa wannan tsari sabo, ko kuwa dai tsarin Imamanci yana da ci gaba mai dorewa?
Tsarin Imamanci, tsari ne na Ubangiji wanda ba ya yankewa kuma ba shi da lokacin tsayawa, yana nan a kowane zamani da kowane fage. Tun daga zamanin Manzon Allah (S.A.W.W) har zuwa yau yana nan a tsaye kuma yana aiki; kuma muddin duniya tana nan, zai ci gaba da kasancewa. Kamar yadda Amirul Muminina (A.S) ya bayyana:
«لَا تَخْلُو الْأَرْضُ مِنْ قائِم لِلهِ بِحُجَّهٍ؛ إِمَّا ظَاهِراً مَشْهُوراً، أَوْ خَائِفاً مَغْمُوراً، لِئَلَّا تَبْطُلَ حُجَجُ اللهِ وَبَیِّناتُهُ.»
"Kasa ba za ta taɓa kasancewa babu wanda zai tashi tsaye saboda Allah a matsayin shaida (Hujjah); ko dai ya kasance a bayyane kuma sananne, ko kuma yana cikin tsoro a boye, domin kada hujjojin Allah da bayananSa su ɓaci kuma su ɓace." (Nahjul Balaga, Hikima ta 147)
Wajibi a kan kowane mutum ya san "Tsarin Imamanci" kuma ya yi imani da shi; a kowane zamani da kowane wuri, mutane dole ne su yi biyayya ga wannan tsari kaɗai.
Kowane mutum dole ne ya fito da shi fili kuma ya ayyana a cikin rayuwarsa da dukkan al'amuransa cewa wane tsari yake yi wa biyayya kuma wace gwamnati yake bi. Dole ne ya bayyana ko ya karbi karkashin shugabancin gwamnatin Allah ko kuma ya amshi gwamnatin Ɗagutu (azzalumai), kuma yayi imani ne da Allah ko da Ɗagutu.
Abin takaici, mafi yawan musulmi ba su ba da hankali da ya dace ba ga wannan batu mai matuƙar muhimmanci, kuma ba su fahimci ma'anar "Wilayah" ba, kuma sun gafala daga muhimmancin wannan bangare nata, wato yin biyayya. Su kuwa waɗanda ke da rikon addini da sadaukarwa sosai, sun takaitu ne kawai ga yin wasu jerin ayyuka na farilla da wajibai da kuma barin abubuwan da aka haramta.
A bisa tsarin mazhabar "Shi'a" wanda yake ɗaukar tsarin Imamanci a matsayin madawwami kuma mai ci gaba, a kowane lokaci da kowane irin yanayi, kasancewa karkashin gwamnatin shari'a wata farilla ce ta asali.
- Gwamnati ta keɓanta da siffar Allah kadai:
«إِنِ الْحُکْمُ إِلَّا لِلّٰهِ.»
- "Ba wani hukunci ba face na (saboda) Allah."
- Kuma Allah kaɗai ne ya kamata a bautawa da yi wa biyayya, kuma biyayya ta kasance tsantsa saboda Shi, mutane kuma su kasance masu ƙasƙantar da kai da mika wuya a gaban gwamnatinSa, mulkinSa da tsarinSa:
«أَمَرَ أَلَّا تَعْبُدُوا إِلَّا إِیَّاهُ.»
"Ya yi umarni da kada ku bauta wa kowa face Shi."
- Wannan shi ne addini madaidaci kuma tabbatacce:
«ذَلِکَ الدِّینُ الْقَیِّمُ.»
"Wannan shi ne addini madaidaci." (Suratu Yusuf, Aya ta 40)
Tsarin Imamanci yana nufin gwamnatin Allah; kuma kasancewa karkashinsa yana nufin mika wuya ga hukuncin Allah, da rayuwa a cikin yankin gwamnatin Allah, da kuma rashin yin imani da gwamnatin da ba ta Allah ba. Saboda haka, babu wani bambanci tsakanin zamanonin da A'imma (A.S) suke nan a raye amma azzaluman da suka ƙwaci gwamnati suka hana su shiga tsakanin lamuran al'umma a hukumance, ko kuma a wannan zamanin na Gaiba al-Kubra da Imam (A.S) yake boye; kowane musulmi dole ne ya bi tsarin Imamanci kaɗai.
Tunda yake aƙida akan tsarin Imamanci wani sashe ne na aƙida akan Tauhidi da gwamnatin Allah da kuma mulkin gaskiya, duk mutumin da ya mutu bai san Imamin zamaninsa ba, ya mutu mutuwar jahiliyya; kamar yadda Manzon Allah (S.A.W.W) yake cewa:
«مَنْ مَاتَ وَلَمْ یَعْرِفْ إِمَامَ زَمَانِهِ مَاتَ میْتَهً جَاهِلِیَّهً.»
"Wanda duk ya mutu alhalin bai san Imamin zamaninsa ba, ya mutu mutuwar jahiliyya." (Biharul Anwar, Juzu'i 32, Shafi na 321)
Kuma tunda yake yin biyayya ga sauran tsare-tsare wani nau'i ne na shirka ta fannin tunani da aiki, Imam Sadiƙ (A.S) ya fada a cikin wani hadisi cewa:
«لَا دِینَ لِمَنْ دَانَ اللهَ بِوِلایَهِ إِمَامٍ جَائِرٍ لَیْسَ مِنَ اللهِ.»
"Babu addini ga wanda ya bauta wa Allah da bin shugabancin azzalumin shugaba wanda ba daga bangaren Allah yake ba (ba Allah ne ya ce a bi shi ba)." (Al-Kafi, Juzu'i 1, Shafi na 375)
Ana iya amfani da waɗannan hadisai wajen fahimtar cewa tsarin Imamanci ba tsari ne taƙaitacce ba, a'a, mai ci gaba ne da ɗorewa kuma bai taƙaitu ga zamanin kasancewar Imam a bayyane kadai ba. Yana nan a kowane lokaci kuma ba zai taba tsayawa ko sokewa ba har abada.
Wannan tattaunawa za ta ci gaba...
An ɗauko wannan ne daga littafin "Amsoshi Goma Akan Batun Imamanci"; wanda Ayatullah Safi Golpayegani ya rubuta - tare da ɗan gyara kadan
Ra'ayinka